1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai sabbin hare-hare a Kharkiv

Binta Aliyu Zurmi
January 11, 2023

Rasha ta kai sabbin hare-hare a Kharkiv da ke gabashin kasar Ukraine, jim kadan bayan ziyarar ministar harkokin wajen Jamus Annalena Bearbock.

https://p.dw.com/p/4Lzss
Ukraine Charkiw | Dmytro Kuleba und Außenministerin Annalena Baerbock
Hoto: Ukrainian Foreign Ministry Press Office/AP/picture alliance

Minista Bearbock da ta kai ziyarar gani da ido, ta sha alwashin Jamus za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine a yakin da take yi da Rasha don kare kanta, sai dai hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Jamus din ke kokarin ja da baya daga alkawarin karin wasu manyan makamai da ta yi wa Ukraine, wanda babban jami'in diplomasiyyar Ukraine ya ce rashinsu na janyo yawan asarar rayukan fararen hula.

A ziyarar ta jiya da Bearbock ta kai. Jamus ta bai wa Ukraine tallafin na'urar wutar lantarki da kudinsu ya kai yuro miliyan 20 da ma wasu injinan samar da intanet da suma kudinsu ya kai yuro miliyan 20.

Yankin Kharkiv dai na daya daga cikin yankunan Ukraine da hare-haren Rasha suka fi yi wa barna.