1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari Kherson

December 24, 2022

Rahotanni daga birnin Kherson na Ukraine na nuni da cewa, mutum 10 sun rasa rayukansu yayin da wasu 58 suka jikkata sakamakon hari ta sama da Rasha ta kai.

https://p.dw.com/p/4LPEg
Ukraine I Birnin Kherson bayan harin da Rasha ta kai
Hoto: Ukrainian Presidential Press Service/REUTERS

A sakon da ya wallafa dauke da hotunan barnar da harin ya yi, shugaba Volodymry Zelensky ya yi Allah wadai da harin tare da bayyana harin a matsayin ta'addanci da aka kaddamar domin jin dadi.

Mataimakin shugaban yankin Yuriy Sobolevskyi ya ce, an kai harin na makami mai linzami ne a kusa da wani kanti da ke tsakiyar birnin.

Gwamnatin Kyiv ta ce Rasha na kara zafafa kai hare-hare birnin Kherson tun bayan da ta kwace ikonsa a watan Nuwamban da ya gabata. Sai dai Rasha ta musanta zargin da ake mata na kai hari kan fararen hula.