Barazanar hari kusa da nukiliyar Ukraine
September 19, 2022Talla
Wani hari da Rasha ta kai da makami mai linzami ya fada kusa da wata tashar nukiliya a kudancin Ukraine a wannan Litinin, sai dai rahotanni sun ce harin bai yi wa tashar nukiliyar wani lahani ba. Ukraine ta baiyana harin da cewa yunkuri ne na ta'addanci.
Harin dai ya fada tazarar mita 300 daga tashar nukiliyar inda ya haifar da wani wagegen rami da ya kai zurfin kafa goma sha uku a cewar kamfanin da ke kula da tashar nukiliyar Energoatom.
Ma'aikatar tsaron Rasha ba ta ce uffan ba a game da batun.