1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rasha ta kai hari a yayin ziyarar Guterres

Ramatu Garba Baba
April 28, 2022

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana takaici kan gazawar Kwamitin Sulhu na Majalisar a shawo kan yakin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4AaOo
Ukraine Kiew | Pressekonferenz Antonio Guterres und Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Efrem Lukatsky/AP/picture alliance

A yayin da ake ci gaba da jin karar fashewa a wasu sassan Kyiv babban birnin kasar Ukraine, Sakatare Janar na MDD Antonio Gutteres yayi wata ganawa da Shugaba Volodymr Zelensky, yana mai baiyana takaici kan yadda Kwamitin Sulhu na majalisar ya gagara kawo karshen yakin da ya janyo asarar rayuka da jefa jama'a da dama cikin halin ha-ula'i in ji jami'in, furucin da ke zuwa bayan gane ma idanunsa ta'asar da rikicin ya haifar a Mariupol.

A nasu bangaren kuwa, masu bincike na kasar Ukraine sun gano laifukan yaki da suka haura 8,000 da ake zargin Rasha ta aikata tun bayan da ta soma mamayar Ukraine, Iryna Venediktova wata mai gabatar da kara a Ukraine ce  ta shaida wa tashar DW hakan. Laifukan sun hada da fyade da azabtarwa dama kashe fararen hula da kuma lalata abubuwan more rayuwa da gwamnati ta tanadar ma 'yan kasa.