Rasha ta kai sabbin hare hare wajen Kyiv
July 29, 2022Talla
Sojojin Rasha sun kai harin makamai masu linzami wani yanki kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine a ranar alhamis a karon farko cikin 'yan makonni da wuce.
Akalla mutane 15 suka jikkata sakamakon harin biyar daga cikin su fararen hula a cewar gwamnan Kyiv Oleksiy Kuleba.
Rahotanni sun ce harin ya lalata wani wuri a arewacin Chernihiv a wani abin da Ukraine din ta baiyana da cewa huce haushi ne sakamakon jajircewar da sojojinta suka yi na hana Rasha samun galaba.
A waje guda kuma hukumomin na Ukraine sun ce sun kaddamar da farmaki domin kwato yankin Kherson a kudancin kasar da Rasha ta mamaye.