1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai sabon hari a gabashin Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
February 10, 2023

Rundunar sojojin saman Ukraine ta ce ta lalata makamai masu linzami guda biyar da Rasha ta yi amfani da su wajen kai hari a yankunan Kharkiv da Zaporizhia. Ba a dai bayar da rahoton asarar rai a wannan harin ba.

https://p.dw.com/p/4NKVw
Fagen yaki na birnin Zaporizhia da ke gabashin UkraineHoto: REUTERS

Kasar Ukraine ta bayyana cewa ta fuskanci wani sabon harin makami mai linzami da jiragen sama marasa matuka daga Rasha, bayan wani rangadin da shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya kai Turai don neman karin makamai daga kawayenta.  Sai dai rundunar sojojin saman Ukraine ta ce ta lalata makamai masu linzami na Rasha guda biyar a yankunan Kharkiv da Zaporizhia. Ba a dai bayar da rahoton asarar rai ba a wannan harin, sai dai cibiyoyin makashi da dama sun lalace.

Tun a watan Oktoban da ya gabata  ne fadar mulki ta Moscow ta rubanya hare-hare a wurare masu mahimmanci na Ukraine, lamarin da ke jefa miliyoyin 'yan kasar cikin tsananin duhu da sanyi na tsakiyar hunturu. Shugaba Volodymyr Zelensky na ci gaba da neman abokansa na Turai da su ba shi makamai masu cin dogon zango da jiragen yaki don samun damar tinkarar kasar Rasha.