Rasha ta kai sabon hari a kudancin Ukraine
September 14, 2022Hukumomin Ukraine sun zargi sojojin Rasha da harba makamai masu linzami guda takwas a birnin Kryvyi Rih na kudancin kasar, da nufin kawo cikas ga samar da ruwa a yankin. Sai dai a cikin wani sako da ya watsa ta yanar gizo, Kirill Timoshenko da ke zama babban jami'i a fadar shugaban kasar Ukarine, ya ce babu farar hula da ya jikkata a harin.
Sai dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya yi alkawarin cimma nasara a yakin da kasarsa ke yi da Rasha, a lokacin da ya ziyarci garuruwa da dakarunsa suka kwato daga hannun sojojin mamaya na Rasha. Idan za a iya tunawa dai, sojojin Moscow sun fuskanci koma- baya bayan da dakarun Ukraine suka yi amfani da motocin sulke da manyan makaman atilari wajen fatattakarsu daga Kharkiv a yankin Arewa maso gabashin kasar ta Ukraine.