1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai wani hari mai muni a Ukraine

October 9, 2022

Wani harin makami mai linzami daga kasar Rasha, ya yi sanadiyyar salwantar mutane da ma jikkatar wasu da dama a yankin Zaporizhzhia na kudancin kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Hxk7
Ukraine-Krieg | Raketenangriff auf Saporischschja
Hoto: Leo CorreaAP/picture alliance

Labarin sabon harin ya zo ne kwana guda bayan karya wani bangare na wata gadar da ta hada kasashen biyu, yankin da Rasha ke matukar amfani da shi wajen safarar makamai zuwa Ukraine.

Harin na wannan Lahadin ya kuma jikkata mutane 49  ciki har da kananan yara.

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, ya bayyana harin wanda shi ne mafi muni da aka gani a yankin a baya-bayan nan, a matsayin wata babbar mugunta.

A ranar Litinin ne Shugaba Putin na Rasha, zai jagoranci majalisar tsaron kasar, wanda zai duba batun da ya shafi karyewar gadar mai muhimmanci ga Rasha a yakin.

Ko a farkon wannan makon ma wani harin ya yi sanadiyyar rayukan mutane 17 a yankin na Zaporizhzhia wanda Rasha ke da'awar kwacewa cikin yankuna hudu na Ukraine.