Rasha ta kori daruruwan Jamusawa daga kasar
May 27, 2023Ana sa rai nan bada jimawa ba Jamusawan da suka hada da jami'an diflomasiya da malaman makaranta da kuma ma'aikatan cibiyar Goethe su fice daga kasar kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta ruwaito.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne dai fadar Kremli ta fito da shirin na rage yawan ma'aikatan da ke yi wa Jamus aiki a kasar da kuma na hukumomin kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyana matakin a matsayin marar tushe da kuma rashin adalci, ko da yake bata bayyana adadin ma'aikatan da abun ya shafa ba. Ana dai ganin matsayar da Rasha ta dauka ya biyo bayan matakin da gwamnatin Berlin ta dauka ne na korar wasu daga cikin jami'an leken asiri na Rasha.
Tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine a watan Fabarairun shekarar 2022, dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatocin Moscow da kuma Berlin.