1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Rasha ta karbe garin Kherson

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2022

Mahukuntan Ukraine sun tabbatar da cewa, dakarun Rasha sun karbe iko da garin Kherson da ke yankin kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/47xMD
Yakin Ukraine da Rasha I Motocin Sojoji a Kherson
Garin Kherson da dakarun Rasha suka yi nasarar kwacewa daga hannun UkraineHoto: REUTERS

Shugaban yankin Gennady Lakhuta ne ya tabbatar da hakan, inda ya nunar da cewa sojojin sun mamaye baki dayan birnin na Kherson da ke da yawan mutane dubu 290 kana ba shi da nisa da yankin Crimea da yanzu haka yake karkashin ikon Rasha. Birnin na Kherson dai na zaman birni na farko da Rashan ta kwace iko da shi, tun bayan kutsen da ta yi a Ukraine. Rahotanni sun nunar da cewa an lalata manyan gine-gine a birnin, yayin da Rashan ke ci gaba da jefa bama-bamai a Kiev fadar gwamnatin Ukraine din.