1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kwace iko da Mariupol

May 23, 2022

Dakarun Rasha sun fara tattare baraguzan gine-gine a ma'aikatar sarrafa karafan Ukraine ta Azovstal, bayan da aka umurci dakarun Ukraine da ke makale a ma'aikatar da su janye.

https://p.dw.com/p/4BiSd
Ukraine | Asow-Stahlwerk in Mariupol
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda dakarun Rashar ke kwashe baraguzan gine-gine yayin da wasu ke amfani da na'urori wajen gano ababen fashewa da aka dasa. A cewar wani jami'in Sojan Rasha da ya nemi a sakaya sunansa, a cikin kwanaki biyun da suka gabata, sun lalata nakiyoyi fiye da 100 a ma'aikatar. 

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai kasar Rasha ta ce rukunin karshe na dakarun Ukraine da ke ma'aikatar ta Azovstal sun mika wuya, ko da yake Ukraine din bata tabbatar da hakan ba. 

Tuni dai aka kawo karshen yaki a birnin na Mariupol, birni mafi girma da Rasha ta kwace ikon tun bayan da ta kaddamar da yaki a kasar Ukraine a watan Fabarairun da ya gabata. Samun cikakken iko da birnin Mariupol zai kara wa Rasha iko da yankunan da suka hada yankin Crimean da Rashar ta kwace ikonsa a shekarar 2014 kana yankin gabashin Ukraine da ke hannun 'yan awaren da ke samun goyon bayan moscow.