SiyasaAsiya
Rasha na son ganin an karfafa yarjejeniyar nukiliyar Iran
March 9, 2021Talla
Da yake bayani a yayin wata ziyara da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa, Ministan harkokin wajen Rashan, Sergei Lavrov, ya ce kwan-gaba kwan-bayan da ke a tsakanin kasashen biyu, zai sa a jima ba a warware matsalar da ta hana ci gaba da aiki da yarjejeniyar ba, ya ce lokaci ya yi da za a dora daga inda aka tsaya don cimma manufar shirin.
Takaita sa ido dai kan cibiyoyin nukiliyar Iran na cikin yarjejeniyar da kasashen duniyan suka cimma a 2015 a birnin Vienna, matakin da ya takawa Iran din birki daga gina tashoshin nukiliya a matsayin makami. Sai dai janyewar Amirka daga yajejeniyar a yayin mulkin Donald Trump, ya fusata Iran fara karya ka'idojin.