Rasha ta rage sayar da makamashin gas
July 27, 2022Masu kula da aikin bututun mai, sun tabbatar da cewa Rasha ta soma rage yawan iskar gas da take fitarwa ta hanyar Nord Stream 1 zuwa Jamus tun daga wayewar garin wannan Laraba. Daman babban kamfanin makamashin gas na Rasha mai suna Gazprom ya sanar da cewa, daga wannan Larabar zai rage yawan makamashin da yake sayar wa kasashen Turai don gudanar da wasu aiyuka na gyara, lamarin da ke barazana ga kasashe kamar Jamus da ke dogara sosai akan Mosko wajen samun makamashin.
Wannan na zuwa ne bayan da Kasashen kungiyar tarayyar Turai ta EU suka amince da yarjejeniyar rage amfani da makamashin gas da kimanin kashi 15 cikin dari da kuma rage dogaro kan makamashin daga Rasha. Batun ya soma tayar da hankali kan tasirin da matakin zai iya yi ga tattalin arzikin nahiyar Turai.