Rasha ta sanya hannu da IAEA domin anfanin Ƙasashe masu tasowa
March 29, 2010Rasha ta sanya hannu da Hukumar dake saka ido wajen hana bazuwar makaman Nukiliya ta IAEA wajen buɗe wata sabuwar tashar sarrafa makamashin Nukiliya domin anfanin ƙasashe masu tasowa a yankin Siberiya. Fatan Hukumar at IAEA shine samar da Ton 40 na man Nukiliya domin anfani ƙasashe masu tasowan, a maimakon barin kowace ƙasa ta kafa tata tashar. Tuni dai Amurka ta bayyana goyon bayan ta ga wannan mataki, wanda tace zai hana ƙasashe irin su Iran fakewa da shirin samun ƙarfin makamashi wajen ƙera makaman Nukiliya. Yanzu haka dai ƙasashen Turai da Amurka naci gaba da matsawa wajen ƙaƙabawa Iran takunkumi, don gane da zargin da suke mata na ƙera makamashin Nukiya. zargin da Iran tasha musantawa. Iran dai ta dage cewar shirin ta na samr da ƙarfin wutan lantarki ne domin cigaban al'umanta.
Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Halima Abbas