1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba dabgabe da barkewar yaki

Zainab Mohammed Abubakar
February 19, 2022

Fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin, ta tabbatar da cewar Shugaba Vladimir Putin ya jagoranci kaddamar da gwajin makamai masu linzami.

https://p.dw.com/p/47Hhi
Konflikt: Russland I Ukraine I Belarus I Präsident Putin
Hoto: Mikhail Klimentyev/SNA/imago images

A yayin da ake ci gaba da zaman dar dar a Ukraine, Rasha ta yi gwajin makamai da suka hadar da masu linzami, a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar yiwuwar barkewar rikici tsakanin wannan kasa mai makaman nukiliya da bangaren yammaci na Turai.

A cewar kakakin fadar gwamnati ta Kremlin Dmitry Peskov a birnin Moscow, Putin ya kaddamar da gwajin makaman a lokacin da shugaban Belarus Alexander Lukashenko da ke ziyara.

Tun a jiya ne dai ma'aitatar tsaron kasar ta sanar da shirin gwajin makaman, domin tabbatar ingancinsu. Kremlin dai da sanar da cewar, an yi gwajin makamai masu linzami na kan kasa da zuwa cikin ruwa.