Gwajin makami mai cin dogon zango na Rasha
April 12, 2023A cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar ta ce wata bataliyar sojojinta ce ta harba makamin daga gurin gwajin makaman kasar na Kapustin Yar kuma makamin ya yi nasarar dira a daidai inda ake so a wani sansanin atsaye da ke kasar Kazakhstan.
Tun a farkon yakin Ukraine dai Rasha ta sanar da yiwuwar yin amfani da makaman Nukiliya idan har ta ji halin matsi kuma ko da a jawabinsa na lokacin cika shekara guda da fara yakin shugaba Poutine ya jaddada wannan aniya tasa yana mai yin kashedi ga fadar Kiev da kawayenta.
A baya bayan nan ma dai shugaba Poutine ya yi ikirarin cewa wadannan makamai kirar karshe da ba sa ji ba sa gani kuma babu wata na'ura da ke iya tare su a halin yanzu, kwakwaran kashedi ne ga duk wasu masu neman yin barazana ga Rasha a game da kudirinta a kan Ukraine.