Rasha ta yi watsi da zargin wargaza Ukraine
April 8, 2014Hukumomin kasar Ukraine na ci gaba da fuskantar gwagwarmayar ballewar birnin Donetsk, a daidai lokacin da masu fafutuka suka kwace madafun ikon gine ginen gwamnati. Sun dai yi ikirarin mallakar 'yancin cin gashin kansu, tare da kira ga shugaba Vladimir Putin da ya aike musu da dakarun Rasha domin mara musu baya da taimaka musu. Tuni dai hukumomin Ukraine suka zargi Rasha da ingiza wannan rikici, a yayin da a birnin Washinton, fadar gwamnatin Amurka ta yi martani da kira ga Moscow da daina kokarin wargaza kasar ta Ukraine. Sai dai tuni Rashan ta yi watsi da zargin, tare da danganta sabon rikicin da rashin halalcin sabbin shugabannin Kiev da ke samun goyon bayan kasashen yammaci. Wannan cece-kuce salon yakin cacar baka dai, na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Rashan ke ci gaba yin dandazo a kan iyakarta da Uktraine.
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman