1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta zafafa kai hare-hare a Ukraine

January 30, 2023

Yayin da Moscow ke zafafa kai hare-hare a Ukraine, shugaba Vodolymyr Zelensky ya bukaci kasashe da su hanzarta bai wa kasarsa tallafin makamai.

https://p.dw.com/p/4Mqpm
Ukraine Soledar Wagner Söldner
Hoto: SNA/IMAGO

Kasar Ukraine ta bukaci kawayenta da su gaggauta ba ta tallafin makamai, yayin da ta ce har yanzu ta na cikin halin tsaka mai wuya. A cikin sanarwar da ya fitar ta kafar bidiyo, shugaba Volodymyr Zelensky ya ce yankunan Bakhmut da Vuhledar da kuma wasu sassan Donetsk na ci gaba da fuskantar hare-haren Rasha, inda gwamnatin Moscow ke zafafa kai hare-hare a yankunan.

Shugaban ya kara da cewa, Rasha na son tsawaita yakin, tare da ganin bayan dakarun Ukraine a don haka akwai bukatar samar da makamai a kan lokaci.

Gwamnatin Kyiv dai ta bukaci tallafin jiragen yaki bayan da Jamus ta amince da tura mata tankokin yaki kirar Leopard 2. Bukatar hakan dai na zuwa ne bayan da aka kai wani kazamin hari a Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine din.