1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta zargi Amurka da dakile sulhu a yakin Ukraine

September 5, 2024

Fadar Kremlin ta fitar da sanarwar cewa babu wata kofar tattaunawa domin kawo karshen gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine a wannan kadami da ake ciki na musayar makamai masu linzami daga bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/4kIAd
Wasu daga cikin sojojin Ukraine a fagen a kan hanyarsu ta zuwa fagen daga a yankin Donezk
Wasu daga cikin sojojin Ukraine a fagen a kan hanyarsu ta zuwa fagen daga a yankin DonezkHoto: ROMAN PILIPEY/AFP/Getty Images

Mai magana da yawun fadar ta Kremlin Dmitry Peskov, shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce sam babu wani shiri na tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu, kasancewar Amurka da kasashen Turai basu da burin ganin an kawo karshen yakin ta hanyar diflomasiyya.

Karin bayani: Yakin Rasha da Ukraine ya dauki sabon salo

Sanarwar fadar ta Kremlin na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Rasha ke ci gaba da zafafa kai hare-hare kan Kiev na Ukraine, inda a gefe guda dakarun Ukraine ke ci gaba da samun horo daga rundunonin sojojin kasa da kasa, domin tunkarar abokan gaba.