1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Vladamir Putin ya ce Rasha tuni ta hango matsalar a Turai

Kamaluddeen SaniSeptember 4, 2015

Vladamir Putin na Rasha ya yi nuni da cewar matsalar 'yan gudun hijirar da ke addabar nahiyar Turai matsalace da tuni aka yi hasashen faruwar ta sakamakon irin manufofin Turai a yakin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1GRFn
D-Day Feier 06.06.2014 Ouistreham Putin Merkel
Shugaban Rasha Vladamir PutinHoto: picture-alliance/dpa

Vladamir Putin na furta wadanan kalaman ne a birnin Moscow akan halin matsalolin bakin haure a nahiyar Turai a inda ya kara da cewar shi a karan kansa ya yi gargadi a dangane da yiwuwar faruwar hakan to amma akai biris da shi.

Ya ce tuni Rasha a shekaru da dama da suka gabata sun bayyana cewar akwai babbar matsala muddin dai kasashen Yammacin Turai suka yi gaban kansu a harkokin yankin Gabas ta Tsakiya.

Vladamir Putin dai na yin wannan kakkausar sukar ce ga manufofin nahiyar Turai kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya da a yayin da ake ci gaba da samun yawaitar 'yan gudun hijira da suka fito daga nahiyar Afrika da Gabas ta Tsakaiya.