1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta ci gaba da rufe gas dinta

September 2, 2022

Bayan sanarwar sake bude bututunsa na iskar gas da ya yi tun da farko, kamfanin samar da iskar gas na Rasha Gazprom ya ce hannun agogo ya koma baya.

https://p.dw.com/p/4GN8f
Deutschland | Pipeline Nord Stream 1
Hoto: Stefan Sauer/dpa/picture alliance

Kamfanin samar da iskar gas mallakin Rasha wato Gazprom, ya ce bututun samar da makamashinsa na Nord Stream 1 zai ci gaba da zama a rufe har sai illa Ma Sha Allahu.

Matakin a cewar Gazprom, ya zo ne bayan samun daya daga cikin injunan kamfanin a kusa da St. Petersburg na yoyo.

A cewar kamfanin na Rasha wanda kasashen Turai ke dogaro kan makamashin da yake samarwa, za a ci gaba da rufe bututun ne domin gano yadda zai maganta tsiyayar da iskar ke yi.

Da ma dai a ranar Asabar ne aka tsara dawo da aika makamashin ta bututun na Nord Stream 1, bayan tsaikon kwanaki uku da aka sanar domin bayar da damar gyara.