Yankunan mamaye na Ukraine sun amincewa da hadewa da Rasha
September 27, 2022An fara kirga kuri'u a yankunan kasar Ukraine da Rasha ta mamaye da aka gudanar da zaben raba gardama na hade yankunan da kasar Rasha. Yankuna hudu da aka yi wannan zaben sun hada da Kherson, Zaporizhzhia, Luhansk da Donetsk. Tuni jami'an yankunan da ke goyon bayan Rasha suka ce samakaon ya nuna cewa galibin mutanen sun amice da matakin hadewa da Rasha. Kafofin yada labaran Rasha suka ruwaito sakamakon kuri'ar kuma da gagarumin rinjaye mazauna yankunan suka amince da hadewa da Rasha.
Kasashen Yamma sun yi tir da matakin sannan sun nuna rashin amincewa da duk wani yunkurin hada yankunan da kasar Rasha, inda a wannan Talata, sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce kasashen duniya ba za su taba daukan yankunan a matsayin wani bangare na kasar Rasha ba.
Rahotanni daga gabashin Ukraine na nuni da cewa dakarun kasar suna ci gaba da samun nasarar kwace yankunan daga hannun sojojin Rasha ciki har da wasu yankunan da aka yi zaben raba gardama. Yayin da dubban 'yan Rasha galibi matasa ke ci gaba da tserewa daga kasar domin kauce wa matakin Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha kan shiga aikin soja, domin neman samun nasara a kutsen da kasar ta kaddamar kan Ukraine.
Mahukuntan kasar Kazakhstan su ce kimanin 'yan Rasha 100,000 suka shiga kasar tun bayan sanarwar shiga aikin soja da shugaban Rasha ya sanar, kana wasu dubban sun shiga sauran kasashen da ke makwabtaka da Rasha.