1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

BRICS: Shirin karbar sababbin mambobi

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2023

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana bukatarsa ta karbar bakuncin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa wato BRICS na gaba, bayan da ya gaza halartar taron kungiyar na bana a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4VV5y
15th BRICS Gipfel in Südafrika
Hoto: BRICS/Handout/AA/picture alliance

Shugaban Vladimir Putin na Rasha ya gaza halartar taron kungiyar na bana da Afirka ta Kudu ke karbar bakunci, sakamakon sammacin kama shi da Kotun Hukunta masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC ta bayar kan zarginsa da aikata laifukan yaki a makwabciyar kasarsa Ukraine. Cikin wani jawabin faifen bidiyo da ya gudanar wanda aka yada kai tsaye a zauren taron kungiyar ta BRICS, Putin ya gayyaci sauran mambobin kungiyar wato Brazil da Chaina da Indiya da kuma Afirka ta Kudu zuwa birnin Kazan domin halartar taron kungiyar na gaba a watan Oktabar shekara ta 2024 da ke tafe.

Afirka ta Kudu | Johannesburg | ​​​​Taro | BRICS | Vladmir Putin | Rasha
Shugaba Vladmir Putin na RashaHoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

A jawabin nasa yayin taron da shugabannin kasashen Chaina Xi Jimping da na Brazil Luiz Inácio Lula da Silva da na Afirka ta Kudu mai masaukin baki Cyril Ramaphosa da kuma firaministan Indiya Narendra Modi ke halarta, Putin ya sake jaddada dalilansa na dakatar da yarjejeniyar fitar da hasti tare da Ukraine da kuma yin kakkauasar suka ga Kasashen Yamma da Kiev din. A yanzu dai shugabannin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa wato BRICS da suka hadar da Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma Afirka ta Kudu, na tattauna batun karbar sababbin mambobi a kokarin da take na samun karfin fada a ji a duniya.