Rasha za ta fara sayar da makamai ga Iran
April 13, 2015Ministan kula da al'amuran tsaron sirri na Isra'ilan Yuval Steinitz ya bayyana hakan inda ya ce wannan na nuni da cewa Iran za ta yi amfani da bunkasar tattalin arzikin da za ta samu sakamakon cimma yarjejeniya kan makamashin nukiliyar tata ta hanyar sayen makamai amma ba kyautata rayuwar al'ummarta ba. Rasha dai ta ce Iran na da damar mallakar makaman kasancewar an cimma matsaya dangane da batun makamashin nukiliyarta da aka yi ta takaddama a kai. Ita ma ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta fito fili ta bayyana rashin gamsuwarta da wannan mataki da Rashan ta dauka, sai dai ma 'aikatar cikin gidan Amirkan ta ce wannan ba zai yi nakasu ba ga kokarin cimma matsayar karshe tsakanin Iran din da kasashe shida masu karfin fada a ji a duniya kan batun makamashin nukiliyar na Iran.