Mali za ta karfafa hulda da Rasha
February 7, 2023Talla
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a wannan Talata ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaki kasashen yankin Sahel na Afirka da suke fama da matsalolin tsaro na kungiyoyin jihadi. Lavrov ya fadi haka yayin ziyarar da ya kai birnin Bamako na kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka. Ministan ya ce Rasha za ta taimakin kasashen domin shawo kan matsalolin da suke ciki.
A shekara ta 2020 sojoji suka kwace madafun ikon Mali inda suka karkata hulda daga Faransa wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka zuwa kasar Rasha. Tun shekara ta 2012 kasar ta Mali ke fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyi tsgaeru masu dauke da makamai da masu ikirarin jihadi.