1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na tilasta wa 'yan kasa shiga aikin soja

Ramatu Garba Baba
September 25, 2022

Duniya na sukar gwamnatin Rasha kan shirinta na tilasta wa ‘yan kasa shiga aikin soji a kokarin da take na karfafa rundunar da za ta karasa aikin mamayar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4HJGu
Moskau Proteste Mobilisierung Verhaftung
Hoto: Alexander Nemenov/AFP

Jami‘an tsaron Rasha sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na tura wadanda shekarunsa suka isa zuwa fagen daga a yakin da take da Ukraine. Rahotanni na cewa an kama mutum fiye da dubu daya ciki har da yara kanana, baya ga haka jami'an tsaron na kamen wadanda suka yi yunkurin tserewa daga kasar don kada su shiga aikin soja kamar yadda gwamnati ta nemi a yi.

Zanga-zangar da ta barke a ranar Asabar da ta gabata, ta kasance mafi girma da aka yi bisa adawa da yakin Ukraine a cikin Rasha, boren ya barke jim kadan da jawabin Shugaba Vladimir Putin na neman ‘yan kasar, su shiga aikin soji don karfafa rundunar sojin kasar da ke kokarin mamaye Ukraine. Wannan batu ya kuma janyo wa Kremlin suka musamman daga Shugaba Volodymr Zelensky na Ukraine da ke cewa, Putin na tura matasa zuwa ajalinsu.