1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Zargin 'yan Ukraine a yankin Belgorod

Binta Aliyu Zurmi
May 23, 2023

Rahotanni daga kasar Rasha na cewar gwamnan yankin Belgorod ya ce suna aikin kakabe masu yi musu zagon kasa a yakin da suke ci gaba da gwabzawa da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Rh4D
Russland l Stadt Belgorod
Hoto: Polina Nikolskaya/File Photo/REUTERS

Gwamna Vyacheslav Gladkov ya ce da taimakon ma'aikatar tsaron Rasha gami da wasu hukumomi suna bin gida-gida domin kakabe wasu da suke zargin 'yan Ukraine da suka kutsa yankin da ke kan iyakar Rasha da Ukraine.

Mahukuntan yankin sun ce an sami mutuwar wata mata guda da ma jikkatar wasu, sai dai mutanen da suka tsere daga yankin ba za su iya komawa ba a yanzu har sai sun kammala abin da suke yi.

Watanni 15 ke nan kasashen Rasha da Ukraine suka kwashe suna fada da juna inda Rasha ke kara matsa kaimi na ganin ta kwace wasu garuruwan Ukraine musamman daga yankin gabashin kasar.

Ko a jiya Litinin Rasha ta kai farmaki cikin dare da makamai masu linzami a kan garin Dnipro.