1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha zata fuskanci sabon takunkumi

July 28, 2014

Kasashen Turai da Amirka sun amince kan daukan sabbin matakan takunkumi kan Rasha, bisa zarginta da suke na kin taka wa 'yan awaren Ukraine birki.

https://p.dw.com/p/1CksA
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a gabacin kasar Ukraine tsakanin dakarun gwamnatin kasar da 'yan awaren gabacin kasa, shugabannin kasashen Faransa, Jamus, Britaniya,Italiya da kuma Amirka, sun tabbar a yau din nan Litinin da aniyar su ta daukan wasu sabin matakan takunkumi kan Rasha, ganin yadda lamurran kasar Ukraine ke gudana a halin yanzu a cewar fadar shugaban kasar Faransa, cikin wata sanarwa da ta fitar, inda suka ce duk da kiraye-kirayen da suka yi wa Rasha na ta tsawata 'yan awaren gabacin kasar ta Ukraine, amma bisa dukkan alamu bata yi komai a kai ba.

Sai dai a cewar hukumomin kasar ta Rasha ta bakin Sakataran harkokin wajan kasar Sergueï Lavrov, matakkan tsaurara takunkumi kan Rasha, abu ne da ba zai yi tasiri ba, inda kuma ya kara da cewa yana mai tabbatar musu cewa Rasha zata jure duk wasu wahalhalu da zasu iya kunno kai cikin tattalin arzikin ta.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar