Rashin hadin kan 'yan adawa a Kamaru
August 22, 2018Abin da ya sanya wasu masu lura da siyasar kasar ta Kamaru ke ganin ko a wannan karo Shugaba Paul Biya shi ne zai lashe zaben matsawar 'yan takara na bangaren adawa suka shiga zaben baram-baram.
'Yan takara takwas ne dai za su fafata da Shugaba Biya a zaben na ranar bakwai ga watan Oktoba mai zuwa wanda zai gudana a zagaye daya tilo. Kuma duk yinkurin da 'yan takara na adawa takwas suka yi ya zuwa yanzu na tsayar da dan takara daya daga cikinsu da zai kalubalanci shugaba mai shekaru 85 da kuma ya share shekaru 35 a kan gadon mulkin kasar ya ci tura.
To sai dai da yake tsokaci kan wannan batu Jean Tsomelu na jam'iyyar adawa ta SDF cewa ya yi da wuya a wannan karo jam'iyyarsu ta amince da batun kafa wani kawancen adawa da zai kalubalanci Shugaba Biya domin a zabukan baya sun sha kafa irin wannan tsari amma daga karshe wani daga cikin shugabannin kawancen ya ci amana.
Wannan zabe na kasar Kamaru na zuwa ne lokacin da kasar ke fama da rikicin 'yan awaren yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi, wanda ke zama babbar kalubalen da ke a gaban sabon shugaban kasar ta Kamaru.
Sai dai baya ga gaza hada kai wuri daya wasu na zargin wasu daga cikin 'yan takara na adawa a kasar ta Kamaru da kasancewa 'yan takara na boge wadanda a zahiri ke yi wa Shugaba Biya aiki ne a fakaice.