1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nawa kasashe ke kashewa kan siyan makamai?

Kersten Knipp ZMA, YB
November 19, 2018

Cibiyar bincike ta kasa da kasa kan zaman lafiya da rigingimu da cinikin makamai a birnin Stockholm na Sweden ta ce kungiyoyin kasa da kasa na fuskantar matsalar samun bayanan kudin da gwamnatoci kan kashe wa makamai.

https://p.dw.com/p/38WuZ
Tschad Armee Boko Haram
Hoto: Reuters/E. Braun

Ba dukkan bayanai ba ne ke isa gaban kungiyoyi da ma hukumomi kamar Majalisar Dinkin Duniya ba. Hakan ba wai yana nufin babu wadannan bayanai ba ne, samun su ne kawai ke da wuya. A cewar cibiyar binciken zaman lafiya da cinikin makaman da ke Stockholm (SIPRI), daga nan sai a buge da hasashen cewar babu bayanan, batu da ke sanya rashin sanin bayanan da ke kunshe da irin kudaden da gwamnatoci ke kashewa kan makamai a wasu yankunan kasashen duniya.

Kasashen Afirka da ke yankin kudu da sahara alal misali za su iya gabatar da bayani game da kudin da suke kashewa a bangaren soji ne kawai a zauren MDD. Sai dai matsalar ita ce, tsawon shekaru uku kenan babu wata guda daya da ke wannan yankin da ta bayyana a gaban MDD domin gabatar da kudaden da ta kashe a bangaren soji. Kuma cikin shekaru 10 da suka gabata kasashe biyar kacal suka yi hakan.

Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule
Yaki ya sanya soja ba zama a kasashe irin Najeriya da KamaruHoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

Nian Tian da ke zama daya daga cikin marubuta sakamakon binciken na SIPRI  ya ce, wajibi ne a samar da wata kafa da za ta karfafa wa kasashen gwiwa na rika gabatar da bayanansu gaban MDD, kasancewa kasashen nada wadannan bayanan.

Bayanai sun nunar da abu guda; cewar ana kashe kudade masu dumbin yawa a fannin tsaro musamman a kasashen Sudan da Afirka ta Kudu da Angola da Najeriya. Kasashen na kashe kashi 1.7 na kudin da kasar ke samu a bangaren soji. A cewar Bankin Duniya,  Jamus ta kashe kashi 1.2 a bangaren makamai a shekara ta 2017.

Gwamnatocin irin wadannan kasashen sun fi kama da zama na kama karya. Kasancewar basa damuwa da bukatun al'ummarsu, sun fi amfani da soji wajen tabbatar da madafan iko kan jama'a kamar yadda Nian Tian ya fada.

Symbolbild Waffenumsätze steigen Waffen Maschinenpistolen MP5
Makudaden kudade ne dai kasashe kan kashe kan mallakar makaman.Hoto: picture alliance / dpa

Bugu da kari rahoton na SIPRI na nuni da cewar ana samun sauyi dangane irin kudaden da ake kashewa a bangaren ayyukan soji a kasashen na kudu da sahara, saboda dalilai guda biyu. Na farko dai koma baya a fannin albarkatun kasa, da kuma karuwar yake yake a yankin.

Faduwar farashin mai wanda ya shafi Najeriya alal misali, ya janyo mata koma baya a kashe-kashen kudi da take. A daya hannun kuma an samu karuwar rigingimu na yaki. A yaki da masu tsananin kishin addini a Mali, rikicin da ke barazanar raba kasar biyu, ya janyo kara yawan kudaden da kasar ke kashewa da wajen kashi 152 bisa 100 zuwa Dalar Amurka miliyan 275 tsakanin 2014-2017.