1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan fitar da hatsin Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
April 25, 2023

kasar Rasha ta sake yin barazanar kawo karshen yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine, bayan zargin Kiev da yin amfani da jirage marasa matuka wajen kai mata hari a gabar tekun Crimea.

https://p.dw.com/p/4QVie
Rasha na barazanar dakatar da fitar da hatsi daga UkraineHoto: dpa/Ukrinform/picture alliance

Makonni uku kafin kawo karshen yarjejeniyar kasa da kasa kan fitar da hatsi daga Ukraine, kasar Rasha ta sake yin barazanar cewar ba za ta sake tsawaita ta ba. Ma'aikatar tsaro a Moscow ta ambaci abin da ta danganta da "hare-haren ta'addanci daga gwamnatin Kiev" a matsayin hujja na neman yin watsi da matakin.

Dama dai Rasha ta zargi Ukraine da yin amfani da jirage marasa matuka wajen kai hari a sansanin jiragen ruwa na tekun Black Sea na Rasha da ke gabar tekun Crimea da ta mamaye a watan Maris da Afrilu. Ita dai Ukraine tana daya daga cikin manyan masu fitar da amfani noma a duniya, inda kasashe matalauta da dama suka dogara a kan hatsi da take fitarwa zuwa kasashen waje.