1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro a Pakistan gabanin zabe

May 9, 2013

Kungiyar Taliban ta yi barazanar kai hare-hare na kunar bakin wanke a lokacin zabubukan gama gari da za a gudanar a kasar ta Pakistan a ranar Asabar mai zuwa.

https://p.dw.com/p/18V0f
Men help injured blast victims arrive at a hospital following a bomb explosion during an election campaign meeting in Kurram tribal district , part of Pakistan's Taliban-infested tribal belt on the Afghan border on May 6, 2013. A bomb tore through a political rally in Pakistan Monday, killing 18 people and wounding 55 in the most deadly attack so far during the campaign for historic elections at the weekend. AFP PHOTO/ ALI AFZAL (Photo credit should read ALI AFZAL/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

A cikin wata wasika da jagoran kungiyar ta Taliban Hakimullah Meshud ya baiyana ya ce ya ba da izini ga 'ya'yan kungiyar domin kai hare-haren a ko-ina cikin kasar domin kawo tsaiko ga zabubukan na gama gari.

Yanzu haka dai wasu 'yan bindiga na yin garkuwa da dan tsohon firamininista Yusuf Raza Gilani wanda suka sace a wajan wani gangamin siyasa a lardin Benjab. Wasu rahotannin kuma na cewar 'yan bindigar sun kashe daraktan yakin neman zabe na Haider Gilani sannan shi kansa ya samu rauni a wani hari da suka kai. Gwamnatin Pakisatan dai ta kudiri aniyar jibge sojoji kusan dubu 90 a yankin arewa maso yammacin kasar domin tabbatar da tsaro a lokacin zabubukan wadanda ke cike da tarihi.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal