1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Aikin jarida ya yi babban rashi

July 2, 2019

A Najeriya ana ci gaba da nuna alhini dangane da rasuwar marigayi tsohon shugaban gidan radiyoyn jihar Kano kana tsohon Janar Manaja na gun-gun gidajen radiyo Freedom da ke Kano Umar Sa'id Tudunwada.

https://p.dw.com/p/3LTYE
Malam Umar Sa’id Tudun Wada (Kano State Radio Corporation, Managing Director, Nigeria) | 09 | Session | Reporting terror: Who sees what, when and why?
Marigayi Malam Umar Sa’id TudunwadaHoto: DW/P. Böll

Tun dai kusan shekaru 40 din da suka gabata ne marigayi Malam Umar Sa'id Tudunwada ya fara aikin jarida a kafafen yada labarai daban-daban musamman gidajen radiyo da talabijin. Ya kasance jajirtacce mai kuma kira da a tsaftace aikin jaridar, tare da horon 'yan jarida da su guji yin karya da kazafi a yayin aikinsu. Babban yayansa Alhaji Yakubu Sa'id Tudunwada ya nunar da cewa tun yana karaminsa yake nuna sha'awarsa ga aikin jaridar.

Ya dai fara aikin jarida da gidan talabijin na NTA a  shekara ta 1980 kafin daga bisani ya koma gidan talabijin na ARTV da ke jihar Kano da sauran kafafen yada labaraio da suka hadar da Freedom Radiyo da Radiyo Kano da Dandal Kura da ke Maiduguri da VOA Hausa da kuma wakilin DW Hausa a Kano.
A lokacin rayuwarsa, Tudunwada ya kasance mutum mai son kyautata hulda tsakaninsa da ma'aikatan da ke kasa da shi da kuma son ganin suma sun ci gaba sun tsaya da kafafunsu, kamar yadda mataimakinsa a lokacin da yake rike da manajan darakta na gidan Radiyo Kano Lawal Isa Bagwai ya shaidawa wakilinmu na Kano Abdulrahman Kabir. Ya nunar da cewa a koda yaushe yana da burin taimakwa na kasa da shi da son ganin ya samu kwarewa ta fuskacin aiki ta hanyar tura ma'aikatansa kwasa-kwasai da bitoci domin inganta aikinsu.

Umar Sa'idu Tudunwada und Abdulrahman Kabir
Wakilinmu na Kano Abdulrahman Kabir tare da marigayi Umar Sa'idu TudunwadaHoto: DW/T. Mösch

Marigayi Umar Sa'id Tudunwada ya rasu sakamakon hadarin mota a ranar Lahadi 30 ga watan Yunin da ya gabata, ya kuma bar mata uku da 'ya'ya 17. Rasuwar tasa dai ta yi sanadiyyar barin gagarumin gibi a fannin aikin jarida, da za a jima ba a cike shi ba.