Rashin wutar lantarki na gigita al'ummar Gao na kasar Mali
March 28, 2024Kusan makonni biyu a garin Gao da ke a arewacin Mali, babu wutar lantarkin, na'urorin samar da wuta na kamfanin wutar lantarki na kasa, EDM, wadanda suke samar da wutar lantarkin sun lalace a cewar hukumomin yankin.
Masu sana'a da 'yan kasuwa suna fama da wannan yanayin a tsakiyyar watan Ramadan, wanda wannan shi ne karon farko a tarihin yankin da ake fama da rashin wutar lantarkin a tsawon lokaci.
Mohammed mai yin aikin walder ya dakatar da aikinsa sannan ma'aikatansa guda biyar ya dakatar da aikinsu saboda rashin wutar lantarkin
"A halin yanzu na rufe wurin aikin, ina gida saboda ina nesa ba zan iya biyan kudi ba na hau motar kasuwa don zuwa wurin aikin da ko ka zo ba ka samun komai .Idan ba aiki, babu kudin hawan mota."
Ainafin dukkanin kayayyaki da dan abin masarufi da aka samu a birnin Gao sun yi tashin gobron zabi. Ma'aikata 15 da aka tura daga Bamako zuwa Gao domin yin aikin gyaran naurorin da ke samar da lantarkin sun kwashe kwanaki suna aiki don magance tabarbarewar injinan janareta da aka girka a karshen shekarar ta 2023 a birnin a cewar Boubacar Dakka Traoré, magajin garin Gao.
"An haɗa sabbin injinan da ake buƙatar haɗawa. Dangane da tsofaffin da ya kamata a yi wa kwaskwarima, an yi musu kwaskwarima. Amma za su daidaita komai."
Yanzu haka kamfanin samar da wutar lantarkin na Gao na yin karba karba na awowi hudu na wutar lantarkin a cikin unguwanni, yanke wutar lantarki ya kai wani matakin inda kusan koi na ne ake cire wutar a kasar Mali.