1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ratko Mladic zai shafe rayuwarsa a kurkuku

Mouhamadou Awal Balarabe
June 8, 2021

Kotun kasa da kasa ta tabbatar da hukuncin daurin rai da rai ga tsohon shugaban sojojin Sabiyawan Bosniya Ratko Mladic, bayan da aka same shi da laifin kisan kare dangi da aka aikata a yakin Bosniya daga 1992 zuwa 1995.

https://p.dw.com/p/3ubcu
Den Haag | Internationaler Strafgerichtshof | Ratko Mladic
Hoto: Peter Dejong/AP/picture alliance


Alkalan kotun da ke birnin The Hague sun yi watsi da gagarumin rinjaye da karar da tsohon janar Mladic ya daukaka bayan hukuncin da aka yanke masa kan rawar da ya taka a kisan Srebrenica, wanda shi ne mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Ratko Mladic na daya daga cikin manyan shugabannin da kotun kasa da kasa ta yi wa shari’a kan laifukan da aka aikata a yake-yaken tsohuwar Yugoslavia, baya ga tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a 2019, da kuma tsohon Shugaban Yugoslavia Slobodan Milosevic, wanda ya mutu kafin a kammala shari’arsa.

 Yakin da aka yi a Bosniya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 100,000, sannan wasu karin miliyan 2 da dubu 200 sun rasa muhallansu.