1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar matasa a zaben shugaban Turkiyya

Usman Shehu Usman
May 12, 2023

Matasa na iya yanke hukunci kan makomar zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Turkiyya yayin da kasar ke fama da tsadar rayuwa

https://p.dw.com/p/4RHcu
Türkei Parlaments- und Präsidentschaftswahlen 2023 | Wahlkampf Erdogan in ANKARA
Hoto: Cagla Gurdogan/REUTERS

A wannan lahadin ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Turkiyya, tsakanin shugaba Recep Tayyip Erdoğan da wasu 'yan takara uku sai dai babban abokin hamayyarsa Kemal Kılıçdaroğlu na wakiltar kawancen jam'iyyun adawa guda shida.

Babban bangare mai tasiri a zaben na bana shi ne bangaren matasa. Turkiyya ta fi ko wace kasa a Turai yawan matasa ‘yan kasa da shekaru 25. Don Haka DW ta zaga Istanbul, babban birnin kasuwancin kasar don jin ra'ayin matasan Turkawa.

Zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin a Turkiyya
Hoto: Murad Sezer/REUTERS

Kuri'ar matasa za ta kasance mai muhimmanci a zabbukan. Za su yanke shawara yadda ya kamata ko za a tsawaita mulkin shugaba Erdoğan zuwa shekaru 30 ko kuma za su sanya Turkiyya karkashin wani shugaba.

Selçuki wani mai ra'ayin mazan jiya a Istanbul ya shaida wa DW cewa galibin matasa masu jefa kuri'a ba su da wata akida ta musamman. Kungiyoyin ba su da wani matsayi fiye da yadda suke yi wa iyayensu.

"Banbanci da ke tsakanin ‘yan adawa da gwamnati, ya yi yawa matuka, babbancin a fili yake. Matasa ba sa jin dadin hakan. Basu damu da kowace akida ba, amma sun fi damuwa da hanyoyin magance matsaloli".

Matasa na taka gagarumar rawa a zaben Turkiyya na 2023
Hoto: Cagla Gurdogan/REUTERS

Abin da zai zama kalubale ga Recep Tayyip Erdoğan shi ne rashin aiki, inda yanzu haka kashi 20 cikin dari na matasa basu da aikin yi ga kuma hauhawar farashin kaya.

Wasu dai sun shaida wa DW cewa yawancin matasa masu jefa ƙuri'a suna son canji, to amma kuma suna game da 'yan adawa da alkawarinsu na inganta abubuwa fiye da yadda yake a yanzu.

‘Yan takara a wannan zaben duk ba matsahi a ciki dukkansu shekarunsu sun ja, domin kuwa shugaba Erdoğan na da shekaru 69 da haihuwa a yayinda babban abokin adawarsa, Kemal Kılıçdaroğlu, ke da shekaru 74 a duniya.