1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar NATO a rikicin Ukraine

Pinado Abdu WabaFebruary 5, 2015

Sakamakon rikicin Ukraine, kungiyar NATO ta girka wata rundunar ko ta kwana dan inganta tsaro a iyakokin kasashen da ke kawancen, musamman na kusa da Rasha

https://p.dw.com/p/1EVzQ
Treffen Nato-Verteidigungsminister in Brüssel 05.02.2015
Hoto: AFP/Getty Images/J. Thys

Kungiyar Kawancen Tsaron NATO na kokarin daidaita lamarin rundunar ko ta kwanan da take neman girkawa a yankunan da ke kawancen, ta kuma tantance yadda ya kamata ta aiwatar da aiyyukanta. Rundunar wacce za a samarda na sama da na kasa da na ruwa za ta kunshi dakaru dubu 30 ne inji shugaban kungiyarNATOn Jens Stolteberg yayin tzaron ministocin tsaron kawancen da ke guda a birnin Brassel na kasar Beljiyam.

A cikin tsarin akwai wata runduna ta musamman da aka ware wacce ta kunshi dakaru dubu biyar, wadanda za a girka a kan iyakan duk kasashen da ke cikin kungiyar kawancen ta NATO. Kawancen ta yi tanadin wannan rundana ta musamman saboda rikicin Ukraine ne domin a tabbatar da kariya ko da Rasha ta yi yunkurin kutsa kai, kuma za a fara tura dakarun a 'yan kwanaki masu zuwa inda ake sa ran farawa da kasashen da ke yankin Baltik wadanda suka hada da Lituania da Estland da Latviya wadanda ke makotaka da Rashar wadanda kuma suke zargin fiskantar barazana daga irin wasu manufofin da Rasha ke aiwatarwa