1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar Pakistan a yaƙi da ta'addanci

May 6, 2011

Ana daɗa samun yawan masu kiran katse dukkan tallafin da Amirka ke ba wa Pakistan bayan kashe Osama bin Laden da dakarun ƙudumbalan Amirkan suka yi a Abbottabad ta Pakistan

https://p.dw.com/p/11AuG
Kakakin gwamnatin Amirka Jay CarneyHoto: dapd

Bisa ga dukkan alamu dai ana fuskantar barazanar gurɓacewar yanayin dangantaka tsakanin ƙasashen yammaci da ƙawarsu Pakistan bayan mutuwar Osama bin Laden, saboda zargin da suke wa Pakistan na ba wa 'yan ta'adda mafaka da ma taimaka musu. To ko mene ne dalilin da ya sanya al'amura suka ta'azzara akan ƙasar ta Pakistan a matakan yaƙi da ta'addancin.

Garin Abbottabad dake ƙarƙashin jerin tsaunuka yana da natsuwa da kwanciyar hankali. Duniya ma dai ba ta da wata masaniya game da wannan gari in banda yanzun. A zamanin baya 'yan ƙasar Pakistan kan ya da zango a garin ne don hutu, amma a yanzu sunansa ya yaɗu a duk faɗin duniya a matsayin mazaunin Osama bin Laden. Mazauna garin na Abbottabad na mamakin kasancewar maƙobicinsu ne mutumin da duniya ke nemansa ruwa a jallo. Akwai ma masu iƙirarin cewar wannan dai wani mataki ne na yaudara daga ɓangaren Amirka. Kazalika a sauran sassa na duniya ma ana mamakin yadda bin Laden zai zauna a wannan yanki tsawon shekaru da dama ba tare da sanin hukumar leƙen asirin Pakistan ba. An dai saurara daga Rangin Dadfar, mashawarcin gwamnatin Afghanistan akan al'amuran tsaro yana mai faɗi cewar:

Da wuya a ce ba a san da zaman bin Laden a yankin ba

Pakistan Terror Haus von Osama bin Laden in Abbottabad
Gidan bin Laden a Abbottabad ta PakistanHoto: dapd

"Wannan shahararren wuri ne kuma mun san cewar da wuya a yi irin wannan ƙasaitaccen gini da zama a cikin yalwa tsawon waɗannan shekarun ba tare da sanin shuagabanni a can sama ba. Ina fatan hakan zata zama darasi ga waɗanda har yau suke neman yin amfani da ta'addanci don cimma buƙatunsu a dangantakar ƙasa da ƙasa."

To ko shin ana iya musulta ƙasar ta Pakistan tamkar wata ƙasa ta 'yan ta'adda. A cikin wata hira da Deutsche Welle tayi da shi, Christian Wagner darektan sashen binciken al'amuran Asiya a cibiyar nazarin kimiyya da siyasa dake Berlin yayi nuni da cewar:

"A'a Pakistan ba 'yar ta'adda ba ce, amma tana fama da matsaloli wajen yaƙi da ta'addanci. Kuma ƙasar tana da gaskiya a game da nunin da take yi cewar ita kanta tana yaƙar 'yan ta'addan. Sai dai kuma duk da haka sojojin ƙasar kan kau da kai daga aika-aikan ƙungiyar Taliban ta Afghanistan a yankunan iyakokinta, saboda fatan da suke yi cewar ta haka zasu samu tasiri akan al'amuran Afghanistan."

Pakistan ta daɗe tana fama da fatara

Bombenanschlag in Faisalabad Pakistan
ungiyoyin 'yan ta'adda masu tarin yawa ke addabar asar PakistanHoto: dapd

Ƙasar ta Pakistan dai ta daɗe tana fama da ƙarancin kuɗi da matsalar taɓarɓarewar al'amuran tattalin arziƙi sakamakon ambaliyar da ta fuskanta kwanan baya da kuma rashin kwanciyar hankalin da ta daɗe tana fama da shi a siyasar ta ta cikin gida. A sakamakon haka duk wani mataki na karya tattalin arziƙin ƙasa da Amirka zata ɗora mata ba zai tsinana kome ba illa ma dai ya ƙara taɓarɓara mawuyacin hali da ƙasar ke ciki kuma ƙungiyoyin ta'adda da aka ƙiyasce yawansu ya kai kimanin 100 a ƙasar su ƙara samun kafar cin karensu babu ba babbaka. An ma ji daga bakin Mohammed Amir Rana ƙwararren masani akan al'amuran tsaro yana mai faɗi cewar:

Akwai ƙungiyoyi sama da 100 a Pakistan

"Yawan ƙungiyoyin ta'adda dake ƙasar Pakistan ya wuce 100, saboda ƙasar tana da yankuna masu yawan gaske na ƙabilu da kuma kudancin Punjab da ba mai iya mayar da su ƙarƙashin ikonsa. Kuma dakarun ƙungiyoyin na samun tallafi ne daga manyan birane na ƙasar. A taƙaice ƙungiyoyin na sha'awar fakewa a Pakistan."

A baya ga haka su kansu al'umar Pakistan ba sa ƙaunar Amirka, a yayinda a ɗaya ɓangaren Amirka da ƙasashen Turai ke buƙatar Pakistan domin cimma nasarar yaƙar 'yan ta'adda da kuma yaƙin ƙasar Afghanistan.

Mawallafi:Kai Küstner/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu