1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Spaniya ta sake kafa tarihi

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
July 15, 2024

Spaniya da Ajantina sun yi nasarar kafa tarihi na kasancewar kasashen da suka fi lashe kofunan gasar kwallon kafar nahiyar Turai da ta yankin Amurka.

https://p.dw.com/p/4iKqT
Jamus | Berlin | UEFA | EURO 2024 | Spaniya | Zakaru
Spaniya ta sake kafa tarihin lashe gasar Euro a karo na huduHoto: Kai Pfaffenbach/REUTERS

Wata guda bayan fara gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Turai da Jamus ta karbi bakunci, birnin Berlin ya dauki nauyin wasan karshe na Euro 2024. Bayan da ta lallasa Ingila da ci biyu da daya, Spaniya ta lashe gasar karo na hudu a tarihinta. Wannan kofin ya bai wa Spaniya damar yi wa takwarorinta na nahiyar Turai zarra a yawan lashe kofin na Euro, inda ta zarta Jamus da kofi gudaa. Ko da yake damarmaki da Spaniya da Ingila suka samu kafin a tafi hutun rabin lokaci ba su taka kara ya karya ba, amma lamura sun sauya bayan da suka dawo filin daga. A mintuna na 47 da fara wasa yaro dan baiwa Lamine Yamal na kungiyar La Roja ta Spaniya ya mika wa amininsa Nico Williams kwallo, shi kuwa bai yi wata-wata ba wajen zura ta a raga. A daya bangare kuwa, Cole Palmer na Ingila ne ya rama wa kura aniyarta a mintuna uku bayan shiga filin, inda Jude Bellingham ya mika masa kwallo a minti na 73 da fara wasa. Sai dai yayin da ake shirin busa uir na karshe ne, Spaniya ta sake samun tagomashi a minti na 86 ta hannun Mikel Oyarzabal lamarin da ya sa ta yi wa kungiyar Three Lions sakiyar da babu ruwa.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere a gasar zakarun Turai da Three Lions ta Ingila ta kasa kai labari, lamarin da ke ci gaba da sanya ta sahun kasashen da ba su taba lashe gasar ba duk da fice da babban lig din kasar wato Premier League ya yi a duniya. Duk da nuna rashin jin dadinsu game da baras da wannan damar da suk yi, amma 'yan wasan Ingila musmaman ma Jude Bellingham bai cire tsammanin lashe kofin kwallon kafa na Turai a karo na gaba ba. Da yawa daga cikin ma'abota kwallon kafa na kasashen da Ingila ta raina a nahiyar Afirka kamar Njeriya sun mara mata baya, domin ta shiga sahun wadanda suka taba lashe gasar Euro. Sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, lamarin da ya sa suka nuna rashin jin dadinsu game da yadda Spaniya ta nuna musu cewar baya ga salon wasa ko a girgije kurna ta fi magarya.

Amurka | Copa America | 2024 l Ajantina | Zakara
Ajantina ta lashe gasar Copa America karo na 16Hoto: Juan Mabromata/AFP via Getty Images

Su ma 'yan yankin kudanci da arewacin Amurka, sun buga wasansu na karshe a birnin Miami  tsakanin Ajantina da Kolombiya da nufin lashe Copa America. An dai samu 'yar hatsaniya sakamakon shiga filin wasa ta hanyar da ba ta dace ba da wasu 'yan kallo suka yi, amma dai kamar yadda aka yi hasashe tun da farko Ajantina ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi bayan karin lokaci, sakamakon kwallo da Lautaro Martinez ya ci a minti na 112 da fara wasan. Wannan shi ne kofi na biyu a jere da kungiyar Albiceleste ta Ajantina ta lashe, bayan lashe kofin duniya na kwallon kafa da ya gudana a Qatar. A jimilce Ajantina ta yi nasarar lashe Copa America sau 16 a tarihinta, lamarin da ya bata damar zarce w Brazil da kofi daya. A yayin da Kolombiya ke a matsayi na biyu, ita kuwa Uruguay ta zo ta uku a gasar kwallon kafa ta Copa America bayan da ta samu nasara a kan Kanada a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Birtaniya | Kate Middleton | Wimbledon | 2024 | Carlos Alcaraz | Zakara
Carlos Alcaraz da ya lashe gasar Wimbledon ta 2024 tare da Gimbiya Kate MiddletonHoto: Alberto Pezzali/AP/dpa/picture alliance

Yanzu kuma sai fagen wasan tennis, inda aka gudanar da wasannin karshe na gasar Wimbledon a karshen mako. A bangaren maza, dan wasan Spaniya Carlos Alcaraz ya yi nasarar kare kambun da yake rike da shi, bayan da ya samu nasara a kan Novak Djokovic da ci shida da biyu da shida da biyu da kuma bakwai da shida. Wannan lashe gasar Grand Slam na hudu da ya yi, ya sa Alcaraz mai shekara 21 kacal fara hasashen yadda makomarsa za ta kasance a nan gaba cikin mayan 'yan wasan na tennis. Wadannan manyan da Carlos Alcaraz yake magana a kansu dai, sun hadar da Roger Federer wanda ke da kambun Grand Slam 20 da Rafael Nadal mai kambu 22 da kuma Novak Djokovic mai Grand Slam 24. A bangare mata na gasar ta Wimbledon kuwa da ci shida da biyu da biyu da shida da kuma shida da hudu ne, 'yar Jamhuriyar Cek Barbora Krejcikova ta lashe wasan na karshe a gaban Jasmine Paolini na Italiya wacce dama ta riga baras da wasan karshe a Roland-Garros a wannan shekara. Wannan shi ne kofin Grand Slam na biyu da Krejcikova ta samu, baya ga na Roland-Garros a 2021.