Rayukan mutane sun salwanta a Chadi
October 20, 2022Daruruwan mutane ne suka fito don gudanar zanga-zangar tunawa da ranar da dakarun soji suka yi alkawarin mika mulki ga gwamnatin farar hula, alkawarin da aka daga zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Shugaban likitocin asibitin birnin Joseph Ampil ya tabbatar wa kamfanin dilancin labaran Faransa AFP cewa, mutanen biyar din sun rasa rayukansu ne sanadiyar harbin bindiga. Hayaki ya turnuku a wasu sassan birnin, yayin da ake jiyo fashewar gurneti na hayaki mai sa hawaye.
Masu boren dai na tada jijioyin wuya ne yayin da majalisar mulkin sojin kasar ke ci gaba da jagorantar kasar, inda aka sake rantsar da shugaban mulkin sojin kasar Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasa a karo na biyu.
An ruwaito cewa, masu boren sun kuma kona hedikwatar jam'iyar sabon Firanministan kasar Saleh Kebzabo.