Rayuwar Jimmy Carter a cikin hotuna
Jimmy Carter da ya taba samun lambar zaman lafiya ta Nobel ya samu gagarumar nasara a ciki da wajen Amurka ta fuskar diflomasiyya. Yana da shekaru 100 lokacin da ya mutu.
Shugaba mai saukin kai
Tsohon manomin gyada, Jimmy Carter ya lashe zaben Amurka yayin da ake badakalar Watergate da yakin kasar Vietnam. Dan jam'iyyar Democrat, ya shaida wa masu zabe cewa ''duk lokacin da kuka fahimci na yi muku karya, ka da ku zabe ni, domin ban cancanta na zama shugabanku ba.''
Magidanci mai adalci
Jimmy Carter ya auri matarsa Rosalynn a shekarar 1946. Ta yi aiki tare da shi a matsayin uwargidan shugaban kasa inda ta rika halatar taron ministoci tana goyon bayan mai gidanta.
Mai manyan abokai
Shugaba Joe Biden da ke hannun dama a wannan hoton, ya yi jimamin mutuwar Carter, yana mai cewa duniya ta rasa ''gagarumin shugaba mai dattaku da jin kan al'umma'', ya kara da cewa ya rasa abokinsa, abin kaunarsa.
Mai wanzar da zaman lumana
Jimmy Carter ya assasa sulhu tsakanin Anwar Sadat na Masar da Menachem Begin na Isra'ila, lamarin da ya sanya aka bude cibiyar Carter Centre a birnin Atlanta. Sadat da Begin sun samu kyautar lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a 1978. A shekara ta 2002, Carter ya lashe kyautar ta Nobel domin gode wa ''kokarinsa na samar da zaman lafiya da sulhu ga rikice-rikicen kasashen duniya.''
Alaka da sarauta
A yayin ziyararsa a fadar Buckingham bisa gayyatar Sarauniya Elizabeth II, Cater, ya sumbaci mahaifiyar sarauniya a matsayin gaisuwa, wani abu da ya saba da ka'idar gidan sarauta.
Adawarsa da 'yan Republican
Carter ya fadi zaben Amurka na 1980 bayan da Ronald Reagan wanda ya lashe jihohi 44 cikin 50 ya lallasa shi.
Zaman doya da manja
Shugaban Amurka Jimmy Carter da shugaban gwamnatin Jamus ta Yamma Helmut Schmidt sun yi zaman doya da manja a diflomasiyyance. A cikin kundinsa, Cater, ya rubuta cewa, daya daga cikin ribar faduwarsa zaben 1980 ga Ronald Reagan ita ce, babu wani abu da zai sake hada shi da Helmut Schmidt.
Dambarwar Gabas ta Tsakiya
Carter ya yi kira ga wadanda suka gaje shi da su amince da Falasdinu a matsayin kasa. Ya kuma yi wani abu mai kama da sukar Isra'ila ta hanyar aza ayar tambaya kan ko alakarta da Falasdinu ta zama ta ''nuna wariya.'' A 2006, ya rubuta littafi mai taken '' Falasdinu: Zaman lafiya ba Nuna Wariya ba.''
Mu'amulla da abokan gaba
A shekara ta 2002, Carter, ya ziyarci Cuba inda ya yi jawabi ta talabijin ga kasar mai mulkin kwamunansanci. Shi ne babban jami'in Amurka da ya ziyarci kasar a tsawon shekaru. A ziyarci wani filin wasa tare da Fidel Castro, shugaban Cuba na wancan lokacin.
Shugaban da ake martabawa
Carter ne shugaban kasar Amurka na 39 kuma mafi tsawon rai a cikin shugabannin Amurkan.
Kungiyar dattijan shugabanni ta "The Elders"
A 2007, Jimmy Carter ya samar da kungiyar The Elders tare da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela. Kungiya ce ta dattijai maza da mata da suka yi amfani da gogewarsu wajen bayar da shawarwari kan rigingimu da hanyoyin magance su da ma bin dokokin kare hakkin dan Adam.
Mutunci ya fi tazarce
Tsohon shugaban kasa Barack Obama ya ce Carter ya yi wa masu zabe alkawarin fadin gaskiya a kowane lokaci, ''kuma ya cika.'' Obama ya fadi a wata sanarwa cewa '' ya gamsu wasu abubuwan sun fi mutunci a kan yin tazarce, abubuwa kamar mutunci da martaba da tausayi'' in ji Obama
Gina wa talakawa gidaje
Carter da matarsa Rosalynn sun gina gidaje domin marasa galihu. Sun kebe mako daya a kowacce shekara domin bunkasa shirinsu na Habitat for Humanity tun daga shekara ta 1984. Sun bayar da gudunmawa lokacinsu da ma karfin ikonsu inda suka yi aiki da masu sa-kai 103,000 a kasashe 14 , suka gina da gyara gidajen talakawa 4,331.
Dattijon arziki
A shekara ta 2023, aka kai shi gidan tsofaffi a mahaifarsa da ke garin Plains na Georgia. Amma duk da haka ya zama shugaban Amurka na farko da ya rayu tsawon shekaru 100 kuma ma har ya samu sukunin kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa na 2024.