Halin rayuwar yaran mayakan IS a Siriya
September 23, 2021A wani sabon rahoto da ta fitar a wannan Alhamis, Kungiyar kare hakkin yara ta Save the children ta ce, yara sama da 62 ne suka mutu a inda ake tsare da su da iyayensu a gidajen yarin kasar Siriya. Kungiyar ta ce, yaran sun mutu ne a sakamakon sakaci da rashin kulawa da lafiyarsu.
Akasarin iyayen yaran, wadanda aka kama ne bayan da suka shiga yakin Siriya da sunan nuna goyon baya ga da'awar Kungiyar IS, Save the children ta soki kasashen Turai da laifin juya musu baya, a maimakon ta maida su gida don ganin an sauya musu tunani daga turbar da suka hau na tallafawa aiyukan ta'addanci da sunan jihadi.
Jamus na daga cikin kasashen Turai da ta kwashe 'yan kasarta kimanin 12 a watan Disambar bara daga Siriya, cikinsu har da yara kanana, sai dai kungiyar ta ce, akwai Jamusawa da dama daga cikin wadanda ake tsare da su a yanzu haka a gidan yarin na al-Hol da Roj da aka tsugunar da tsoffin mayakan na IS.