1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai

Lateefa Mustapha Ja'afar ZMA
June 3, 2024

Kungiyar Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai karo na 15, bayan da ta lallasa Borussia Dortmund da ci biyu da nema a wasan karshe.

https://p.dw.com/p/4gbHI
Real MadridHoto: Carl Recine/REUTERS

An kammala samar da sansanin yin atisaye na kungiyoyin da za su fafata a gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na nahiyar Turai. Kasar Kamaru ta mayar da Marc Brys matsayinsa na mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Indomitable Lions, bayan shugaban Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ya bayar da hakuri.

Rahotanni na nuni da cewa an kammala samar da sananonin yin atisaye, ga kungiyoyin kwallon kafa da za su fafata a gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Kasashen nahiyar Turai wato Euro 2024 da za a fafata a Jamus. Tuni ma dai horas da 'yan wasan Jamus din mai masaukin baki Julian Nagelsmann ya gudanar da taron manema labarai, gabanin wasan sada zumunci da za su yi da Ukraine a wannan Litinin din. Yayin taron manema labaran, Nagelsmann ya yabawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spaniya sakamakon lashe Kofin Zakarun Turai da ta yi, tare kuma da kara kwarin gwiwa ga Borussia Dortmund ta Jamus din da ta gaza kai bantenta a wasan na karshe. 

Champions League - Finale - Borussia Dortmund - Real Madrid - Tor 2 Madrid
Vinicius Junior na Real MadridHoto: Carl Recine/REUTERS

Borussia Dortmund ta Jamus din dai ta sha kashi a hannun kungiyar kasar Spaniyan Real Madrid da ci biyu da nema, duk kuwa da cewa ta rike wuta a zagayen farko na wasan. Sai dai ta yi karkon kifi bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, inda Madrid din ta zura mata kwallaye biyu a mintuna 30 na karshen wasa.

Sai dai duk da wannan rashin nasara da suka yi a filin wasa na Wembley, 'yan wasan na Borussia Dortmund, sun nuna farin cikinsu kan irin jajircewar da suka nuna a wannan fafatawa. Mai horas da 'yan wasan na Dortmund Edin Terzic ya shaidawa manema labarai cewa:

"Ina mai taya Real Madrid murna, amma lallai ba mu ji dadin yadda sakamakon wasan ya kasance ba. Mun taka raar gani, shi ya sa ma muke cikin yanayi iri biyu. Babban abin farin ciki shi ne, duk wanda ya kalli yadda muka murza leda ya san ba mun zo wasan karshe ba ne kawai mun zo ne domin mu lashe kofin. Ina ganin mun yi wasa sosai yadda ya kamata har ma mintuna 15 zuwa 20 bayan an dawo hutun rabin lokaci. Sai dai kungiyar da muka fafata da ita, tana da karfi matuka. Za ka lura da yadda wasan ya kufce mana, wannan abu ne da ya kamata mu koyi darasi a kai. Idan ka lura da yadda wasan ya jigata kowa har su abokan karawarmu, mun yi kokari."

Fußball | Trainer Marc Brys
Me horas da 'yan wasa Marc Brys Hoto: KURT DESPLENTER/picture alliance

Rahotanni daga Kamaru na nuni da cewa, mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Marc Brys ya koma bakin aikinsa. Ma'aikatar Kula da Wasanni ta Kamaru ta nada dan kasar Beljiyam din a matsayin mai horas da kungiyar ta Indomitable Lions a watan Afrilun bana, sai dai a makon da ya gabata an maye gurbinsa da Martin Ndtoungou a matsayin shugaban rikon kwarya bayan da suka yi sa-in-sa da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Samuel Eto'o. Kwanaki biyu bayan faruwar hakan an dawo da shi, bayan Eto'o ya bayar da hakuri kan sabanin da suka samu. Eto'o ya kuma tabbatar da cewa mai shekaru 62 Brys ne, zai jagorancin kungiyar a wasannin share fage na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara ta 2026.

Kungiyar kwallon kwando ta Alahly Benghazi ta Libiya, ta sha kashi a wasan karshe na lashe kofin zakarun kwallon kwando na na nahiyar Afirka BAL karo na farko. Alahly Benghazi dai, ta sha kaye ne a hannun Petro de Luanda ta Angola da ci 94 da 107 a Asabar din da ta gabata. Wannane ne dai karo na farko da aka fafta a wasan karshe, tun bayan fara gasar a shekara ta 2021. Kungiyar Kwalon Kwando ta Amurka NBA, na kan gaba a sawun masu taimakawa wasannin na BAL na Afirka.

USA Tennis 2023 US Open – Tag 14 - Novak Djokovic vs. Daniil Medvedev
Da wasan Tennis Novak DjokovicHoto: ELSA/AFP/Getty Images

Bayan fargabar gaza samun kambunsa na 25 da fitaccen dan wasan nan na Tennis na duniya Novak Djokovic ya shiga a gasar Roland Garros, dan kasar Sabiyan ya farfado bayan da ya samu nasara a Asabar din karshen mako da ci bakwai da biyar da shida da bakwai da biyu da shida da kuma shida da nema a kan abokin karawarsa Lorenzo Musetti a gasar French Open. Wannan nasar dai ta nuna irin kwarewa da jajircewar dan wasan, wadda ta sanya shi yin fice a duniya a fagen kwallon Tennis.