1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice ta ce zata yi shawarwari masu tsauri a Gabas Ta Tsakiya

July 29, 2006
https://p.dw.com/p/Buok

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice, wadda ke kan hanyar ta ta komawa yankin GTT ta ce zata gudanar da tattaunawa mai zafin gaske a kokarin kawo karshen fadan da ake yi tsakanin Isra´ila da Hisbollah. A kan hanyarta daga Malaysia zuwa Isra´ila Dr. Rice ta ce ba zata ba da wani wa´adi bisa manufa ba. To amma a tattaunawar da zata yi da shugabannin Isra´ila zata matsa lamba don ganin an cimma wata matsaya game da ka´idojin tsagaita wuta. A kuma halin da ake ciki kasashen duniya na kara matsa kaimi wajen girke dakarun kasa da kasa a Libanon. Yanzu haka dai babban sakataren MDD Kofi Annan ya gayaici kasashe da dama zuwa New York inda za´a shawarta game da shirin kafa rundunar kiyaye zaman lafiya.