1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice ta isa a Isra´ila a mataki na gaba na rangadin da take kaiwa Gabas Ta Tsakiya

November 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvLF

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta sauka a Isra´ila a wani sabon yunkuri na farfado da shirin samar da zaman lafiya yankin GTT wanda har yanzu yake tanga-tangan watanni biyu bayan janyewar Isra´ila daga Zirin Gaza. Rice ta isa Isra´ila ne daga Saudiya a mataki na 4 na rangadin yankin GTT. A Saudiyar ta bayyana warware rikicin Isra´ila da Falasdinawa da cewa yana daya daga cikin muhimman batutuwan da aka sa gaba yanzu. Rice ta fadawa wani taron Isra´ila da Amirka cewa shakka babu yankin GTT zai samu kwanciyar hankali idan aka kafa wata kasar Falasdinawa mai bin tsarin demukiradiyya wadda kuma zata zauna lafiya da Isra´ila. A gobe litinin zata gana da FM Isra´ila Ariel Sharon sannan daga bisani ta zanta da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas.