Amazon na fuskantar turjiya daga kabilun Afirka ta Kudu
April 26, 2022
Yan kabilar Khoi da 'San' na da'awar cewa ana gine-gine akan kasar da suka gada tun kaka da kakanni da ya ratsa tsakiyar gundumomi masu muhimmanci na Cape Town a Afirka ta Kudu. To amma babban kamfanin sayar da kaya ta yanar gizo na Amazon ya kuduri aniyar gina hedikwatarsa a mahadar kogunan Black River da Liesbeek River, da mutanen yankin ke dauka da daraja.
A yanzu dai wata babbar kotu a Cape Town ta dakatar da aikin har sai an shigar da mutanen karkarar 'yan asali da abin ya shafa cikin lamarin. Kabilun dai na bukatar a dakatar da aikin ne dungurungum wanda Amazon ya tsara kashe zunzurutun kudi Euro miliyan 260.
Braley van Sitters wani dan gwagwarmaya na kabilar Khoi ya ce "ba mu yarda ba mu amince ba da wannan aiki.'' Yana ganin ci gaba da kokarin gina ofis din Amazon a wurin bayan jama'ar yankin sun nuna illar hakan ga al'adunsu, rashin martabawa ne ga al'ummomin Afirka ta Kudu.
A can baya dai wannan wuri an yi amfani da shi a matsayin wurin wasan kwallon Golf na kungiyar River Club. A taswirar da aka tsara a yanzu za a gina gidajen kwana da kantuna da kuma ofisoshi sannan da hedikwatar kamfanin na Amazon a filin.
Mutane 1,000 ake sa ran za su samu aikin yi idan har aka samu hedikwatar ta Amazon a yankin. Wannan mataki ya zo daidai da kudurin Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na kokarin jawo masu zuba jari a cikin kasar domin samar da ayyukan yi.
Kamfanin da ke aikin a cikin wata sanarwa ya ce galibin yan al'ummar 'Khoi' da 'San' suna goyon bayan ayyukan da ake yi. Domin karrama al'ummomin, Amazon ya ce sun tsara gina katafariyar cibiyar yada labarai da gandun raya al'adu da kuma dakin wasanni da taruka.
"Tsirarun mutanen da ke adawa da aikin na yada karya game da ayyukan da ake yi da tasirinsa ga rayuwar al'umma da kuma zamantakewar tsirrai da sauran hallitu.'' in ji sanarwar da kamfanin na Amazon ya fitar.
Idan har kotu ta kammala ta janye dakatarwar da ta yi a kan ginin, ana sa ran kammala kashin farko na ginin cikin shekaru biyu masu zuwa. Sai dai a yanzu masu fafutuka sun ce za su ci gaba da gwagwarmaya domin kare kasarsu da kuma al'adunsu.