1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimu da cin zarafin 'yan adawa sun karu a Masar inji Amnesty

January 23, 2014

Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa Masar ta shiga wani yanayi na tashe-tashen hankula maras misali, tun bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi.

https://p.dw.com/p/1AvsP
Ägypten Wahlen
Hoto: Reuters

Amnestin ta yi wannan furici ne a wani rahoto da ta fitar a wannan Alhamiss, inda rahoton ya kara da cewa magabatan na kasar Masar na nuna wariya ne ga bangaren 'yan adawa sannan basa mutunta hakkokin dan Adam, tare da bada shaidar kame-kamen mutane, da hana fadar albarkacin baki da ma hana 'yancin zanga-zanga.

An fitar da wannan rahoto ne kwanaki biyu kafin ranar cikon shekarar soma zanga-zangar da ta yi sanadiyar tumbuke tsohon shugaban kasar Hosni Moubarak a watan Fabrairun 2011.

A kalla dai mutane dubu da dari hudu ne suka mutu tun bayan da babban Hafsan Hafsoshin kasar ta Masar Janar Abdel Fattah al-Sissi, ya hambare Mohamed Morsi daga karagar mulkin kasar, wanda kuma ana iya danganta mace-macen wadannan mutane da amfani da karfin da jam'iyan tsaron kasar ke yi kan masu zanga-zanga.

Rahoton ya kara da cewa mutane da dama ne kuma suka rasu ran 14 ga watan Agusta, bayan da sojoji suka farma masu zanga-zanga ta amfani da jirgin dankaro tare kuma da harbi da harsasai na gaskiya dan tarwatsa su.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal