Rikcin majalisar Nijar ya dauki wani salo
May 21, 2014'Yan sandan Nijar ba su bayyana laifin da ake zargin 'yan majalisar dokoki ukun da aikatawa ba. Amma dai an zabesu ne karkashin lemar jam'iyyar Africa Modem Lumana ta kakakin majalisa Hama Amadou. Saboda haka ne wasu masharhanta ke ganin cewa, wannan mataki ba zai rasa nasaba da rikicin da ke tsakanin bangaren kakakin majalisar ta Nijar da kuma bangaren shuagaban kasa na. Idan dai za a iya tunawadai bangaren gwamnati ta yi ta yunkurin tsige Hama Amadou daga mukaminsa, lamarin da ya kawo tafiyar hawainiya a harkokin tafiyar da majalisar ta dokokin Nijar.
Daukacin 'yan majalisun Jamhuriyar Nijar sun ki amincewa jami'an 'yan sanda sun saurari takwarorinsu Djafarou, Alkali da karimou na Modem Lumana. Suna masu cewa kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar bai amince wani dan majalisa ya fuskanci shari'a ba matikar ya na da rigar kariya.
So daya ne dai a Jamhuriyar ta biyar aka tsare dan majalisa saboda ya burma ma wani taliki wuka. Da ma dai a irin wannan hali ne kawai dokar Nijar ta amince a hukunta dan majalisa ba tare da kwabe masa rigar kariya ba.
Sai dai kuma wani dan majalisar dokoki ya nemi wadanda 'yan sanda suka aiko wa sammace, da su je su amsa kira ko dno wanke kansu.
Mawallafi: Mahaman kanta
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe