Ana samun yamutsi a jam'iyyar shugaban kasar Nijer
October 14, 2015A jamhuriyar Nijer, wani sabani ya kunno kai a tsakanin magoya bayan jam'iya mai mulki ta PNDS Tarayya da kuma jagororin jam'iyar biyo bayan shawarar da aka ce shugaban kasa ya bada na a bari daukacin 'yan majalisar dokokin jam'iyar su wuce ga neman takara ba tare da sun bi matakin tankade da rairaye ba, abun da ya fusatar da wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar.
Wannan sabanin dai ya dauko asalinsa ne tun bayan da jagororin jam'iyyar suka bayana sakon daga shugaban kasa na bukatar ganin 'yan majalisar dokokin jam'iyyar su yi tazarce. Wannan dai ba karamin kalubale ne ba idan har ta tabbata hakan inji Alhaji Nasiru Musa wani dan jam'iyar.
Su ma dai mutanen karkara sun nuna rashin gamsuwarsu kamar yadda Atta Maranga shugaban matasa na PNDS Tarayya reshen Buza ya bayyana.
To amman ga malam Hamissu Dan Malam, jigo a jam'iyar ta PNDS reshen Kwanni, masu nuna bacin ran nasu sun yi gaugawa.
Amma a cewar Dan baba Maman Tsini, kakakin jam'iyar ta PNDS Tarayya na kasa, ya ce babu kanshin gaskiya a wannan labarin da ake zargin shugaban kasar da yi.