Rikici na kara kamari a kasar Ukraine
January 16, 2014Talla
'Yan adawar kasar dai na ganin wannan doka da kotun ta samar a matsayin wani sabon yunkuri da gwamnatin kasar ke yi, na murkushe masu zanga-zanagr da suka mamaye dandalin 'yanci na birinin Kiev din da karfin tuwo.
Rahotanni sun bayyana cewa daga ranar takwas ga watan Maris mai zuwa ne, dokar za ta fara aiki. Masu zanga-zangar dai na neman shugaban kasar Viktor Yanukovych ya sauka daga mukaminsa, biyo bayan kin sanya hanu kan yarjejeniyar kasuwanci ba tare da haraji ba da kungiyar Tarayyar Turai da ya yi. Inda a maimakon haka ya kara karfafa dangantakarsa da kasar Rasha.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman